12 Agusta 2020 - 09:57
Iraqi Ta Dakatar Da Ziyarar Mininstan Tsaron Kasar Turkiya, Bayan Wani Hari Da Ya Kashe Sojojinta

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta yi tir da kakkausar murya akan wani mummunan hari da sojojin Turkiya su ka kai a cikin kasar wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin kasar ta Iraki biyu.

ABNA24 : Sojojin biyu na kasar Iraqi sun rasa rayukansu ne a sanadiyyar wani hari da jiragen yakin Turkiya suka kai a yankin Arbil na kasar Iraki.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iraqi ta dakatar da ziyarar da aka shirya cewa ministan tsaron Turkiya zai kai kasar a gobe Alhamis, sannan kuma tana shirin gayyatar jakadan Turkiyan domin ya amsa tambayoyi akan abinda ya faru.

Ita ma fadar shugaban kasar Iraki ta fitar da bayani da a ciki ta yi tir da harin na Turkiya akan yankin na Kurdawan kasar.

Sojojin kasar Turkiya dai suna kai hari ne a cikin kasar Iraqi a yakin da suke yi da kungiyar kurdawa ta PKK wacce suke dauka a matayin ta ‘yan ta’adda.

342/